Abdullahi Dan Abbas yana bada labarin cewa Annabi ya tsaya yana mai Huduba ranar bude Makka, sai ya ce Babu wata sauran Hijira yana nufin daga Makka; don ta ama garin Musulunci, sai dai kawai Jihadi yana nan kuma yayi Umarnin duk wanda ake nemi ya fito zuwa Jihadi to ya futo don nuna biyayya ga Allah da Manzonsa da kuma Jagora, sannan yai bayanin Haramcin Makka, kuma ya ambaci cewa wannan haramcin tun lokacin da aka halicci sammai da kasa ya kekuma ba'a taba halastawa wani ita ba kafin Annabi, kuma ba zata taba halatta ga kowa ba kuma bayansa kuma shima an halasta masa ita ne wani Dan lokaci na rana sannan kuma Haramcin ya kuma dawowa, sannan kuma ya sake fadin haramcin Makka kan cewa ba'a sare kayar ta kuma ba'a korar Farautar ta kuma ba'a tsintar tsintuwar ta sai ga wanda zai shelanta ta kuma ba'a yankar ciyawarta sai dai an iyakance jemarta sabida bukatar Mutanen Makka.