Ibnu Abbas - Allah Ya yarda dasu - ya cewa Aɗa'u ɗan Abi Rabah: Shin bana nuna maka wata mata daga cikin 'yan aljanna ba? Aɗa'u ya ce: Eh, ya ce: Wannan baƙar matar mutuniyar Habasha, ta zo wajen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ta ce: Lallai cewa ni ina da cutar farfaɗiya kuma cewa ni ina yin tsirara wani abu yana yayewa daga jikina alhali ni ban sani ba, to ka roƙamin Allah Ya yaye mini, ya ce: Idan kin so ki yi haƙuri aljanna ta tabbata gareki, idan kuma kin so zan roƙa miki Allah Ya yaye miki, ta ce: To zan yi haƙurin, sannan ta ce: To ka roƙamin Allah kada in sake yin tsirara idan na yi farfaɗiya, sai ya roƙa mata Allah.