explain-icon

Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayanin cewa ita duniya da abin da ke cikinta wani abu ne da za a ji dadi da shi, na wani lokaci sannan ya wuce, to, mafificin jin daɗinta shi ne mace ta gari, wacce idan ya kallaceta za ta faranta masa, idan kuma ya umarceta za ta yi masa biyayya, idan ba ya nan za ta tsare shi a kanta da kuma dukiyarsa.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Halaccin jin daɗi da abubuwa na halak a duniya wanda Allah Ya halatta wa bayinSa ba tare da ɓarna ko gadara ba.
  • Kwaɗaitarwa a kan zaɓin mace ta kwarai, domin taimako ce ga mijinta wajen biyayya ga Ubangijinsa.
  • Mafificin jin daɗin duniya shi ne abin da ya kasance a kan bin Allah, ko ya taimaka a kan hakan.