Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa duniya mai zakice a abubuwan zaki, kuma koriya a abin gani, sai mutum ya rudu da ita ya yi zari a cikinta ya kuma sanya ta mafi girman himmarsa. Kuma cewa Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka - ya sanya shashinmu zai maye gurbin sashi a wannan duniyar, dan ya duba ya zamu yi aiki, shin zamu tsaya da biyayyarSa, ko zamu saba maSa? Sannan ya ce: Ku kiyayi jin dadin duniya ya rudeku da kawarta, sai ya doraku akan barin abinda Allah Ya umarceku da shi, da kuma afkawa a cikin abinda ya haneku daga gareshi. Daga mafi girman abinda ya wajaba a kiyaya daga gare shi daga fitintinun duniya (su ne) mata, cewa ita ce farkon fitinar da Banu Isra'ila suka afka a cikinta.