Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wata rayuwa ta haƙiƙa sai rayuwar lahira, a cikin yardar Allah da rahamarSa da kuma aljannarSa; domin rayuwar duniya mai gushewa ce, rayuwar lahira kuwa ita ce dawwamammiya mai wanzuwa, sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'ar gafara da girmamawa da gyaruwa ga mutanen Madina waɗanda suka kawo ɗauki ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da Muhajirun, suka taimakesu, suka raba musu dukiyoyinsu, kuma (ya yi addu'a) ga Muhajirun waɗanda suka bar gidajensu da dukiyoyinsu suna neman falala daga Allah da kuma yarda.