explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa dattijo yana girma jikinsa yana rauni, sai dai zuciyarsa budurwa ce akan son abubuwa biyu: Na farko: Son duniya da yawan dukiya. Na biyu: Tsawon rayuwa da shekaru da buri.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Bayanin abinda aka halicci mutum a kansa, shi ne son duniya da tsawon buri.
  • Nuni akan zargin yawan buri, da kwaɗayi akan tara dukiya, hakan yana hukunta tanadi ga mutuwa da falalar sadaka ga mawadaci, da kamewa ga talaka.
  • Mafi soyuwar abubuwa ga ɗan Adam shi ne ransa, shi mai kwaɗayi ne a akan wanzuwarsa, saboda haka sai ya so tsawon rayuwa, kuma ya so dukiya; domin cewa shi yana daga mafi girman sabubba a dawwamar lafiya da jin daɗi, a duk lokacin da ya ji kusancin ƙarewar hakan sai sonsa gare shi ya tsananta, da kuma kwaɗayinsa a kan dawwamarsa.