Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana miji ya ki matarsa ƙin da zai kai zuwa ga zalinci da barinta da bijire mata; Domin mutum an halicce shi ne akan tawaya, idan ya ki wata mummunar ɗabi'a daga gareta, to zai samu wata kyakkyawar ɗabi'ar a tare da ita; sai ya yarda da mai kyan da ta dace da shi, kuma ya yi haƙuri akan wadda bai yarda ba ta munanar, abinda zai sa shi ya yi haƙuri kada ya ki ta ƙiyayyar da zata ɗauke shi akan rabuwa da ita.