Tabi'i Malik ɗan Aus yana bada labari cewa shi ya kasance a wurinsa akwai zinarai, kuma yana son ya canja su da azirfofi, sai Ɗalha ɗan Ubaidullahi - Allah Ya yarda da shi - ya ce masa: Ka bamu zinarenka dan na gansu! sannan ya ce da shi bayan ya yanke zai saya: Ka je Ka dawo, idan ɗan aikinmu ya zo bayannan dan mu baka dirhamomin, Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya kasance yana halarce a wurin, sai ya yi inkarin wannan nau'in na mu'amala, kuma ya yi wa Ɗalha rantsuwa akan cewa ya bada azirfar a take, ko ya dawo masa da zinarensa wanda ya karba daga gare shi, kuma ya bayyana masa sababin hakan cewa Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci cewa saida zinari da azirfa ko akasin hakan ya wajaba ya zama hannu da hannu nan take, inba haka bafa to wannan cinikin zai zama riba abin haramtawa, kuma bataccen ciniki, ba'a saida zinari da azirfa ko azirfa da zinari sai hanuu da hannu kuma karba ya tabbata, haka ba'a saida alkama da alkama ko wake da wake ko sha'ir da sha'ir ko dabino da dabino sai daidai wa daidaida awo da awo,