Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana hanyar yin inagntaccen ciniki a cikin nau’ukan da riba take shiga cikinsu (abubuwa) guda shida sune: Zinare, da azirfa, da alkama, da sha'ir, da dabino, da gishiri, idan sun kasance daga irin nau'in ne kamar saida zinare da zinare azirfa da azirfa... to babu makawa daga sharuɗɗa biyu: Na farko: Tabbatar daidaituwa a cikin awon sikeli ne, idan ya kasance abin aunawa ne na sikeli kamar zinare da azirfa, ko samun daidaito a awo idan ya kasance abin aunawa ne na kwano kamar alkama da sha'ir da dabino da kuma gishiri. Na biyu: Mai siyen ya karɓi abin siyarwar shi kuma mai siyarwar ya karɓi kuɗin, hakan (ya zama) a gurin da akayi cinikin. Idan waɗannan nau’ukan suka saɓa kamar saida zinare a bada azirfa, da dabino a bada alkama misali, to cinikin ya halatta da sharaɗi ɗaya, shi ne mai siyarwar ya karɓi kuɗin shi kuma mai siyen ya karɓi abin siyan a gurin da aka yi cinikin, inba haka bafa to cinikin ɓatacce ne, kuma sun faɗa cikin ribar da aka haramta, mai siyen da mai siyarwar duk ɗaya ne a hakan.