Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya rasa Sabitu Dan Ƙais - Allah Ya yarda da shi - ya yi tambaya game da shi (ya yi cigiyarsa), sai wani mutum ya ce: Ni zan samo maka labarinsa, da dalilin fakuwarsa, sai ya tafi wurinsa sai ya same shi yana cikin baƙin ciki yana mai sunkuyar da kansa a gidansa, sai ya tambaye shi : Meke damunka? sai Sabitu ya ba shi labarin abin da ke tare da shi na sharri; domin cewa ya kasance yana ɗaga sautinsa sama da sautin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma haƙiƙa Allah Ya yi alkawarin narko daga aikata hakan da ɓacin aikinsa, kuma cewa shi yana daga 'yan wuta! Sai mutumin ya dawo zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya sanar da shi da hakan, sai Annabi - tsaira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umarce shi ya koma wa Sabitu ɗan Ƙais ya yi masa albishir da cewa shi ba ya daga 'yan wuta, sai dai yana daga 'yan aljanna, domin cewa ya kasance mai babbar murya ne a halitta, domin shi ya kasance mai huɗubar Manzon Allah ne - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -. kuma mai yi wa mutanen Madina huɗuba.