Sa'ad Bn Abi Waqqas -Allah ya yarda da shi- ya zo Majalisin Annabi SAW yayin da Manzon Allah SAW ya ganshi sai ya ce: Wannan Kawu na ne kuma ina Alfahari da shi, to kowane Muyum ya nuna mun Kawun sa; don ya bayyana a lokacin babu wanda yake da Kawu kamar kawuna, kuma Sa'ad ya kasance daga Qabilar Bani Zahra ne, kuma Mahaifiyar Manzon Allah SAw Amina ita daga Bani Zahra ta ke, kuma shi Xanuwanta ne, kuma 'Yan Uwan Uwa Kawunnani ne.