Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya yi masa magana a kan wani al'amari nasa, sannan ya ce: "Allah Ya so kaima ka so", sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi masa inkarin wannan maganar, kuma ya nusar da shi cewa hada mashi'ar abin halitta akan mashi'ar Allah da Waw shirka ce karama, ba ya halatta ga musulmi ya furtata, sannan ya shiryar da shi magana ta gaskiya: "Allah Ya so Shi kadai", sai ya kadaita Allah a Son Sa, kada ya hada mashi'ar (ganin damar) wani akansa ta kowanne nau'i daga nau'o'in hadawa .