Buraida yana bada labari cewa Annabi idan ya aika Runduna ko tawagar yaki don yakar kafirai yakan nada musu shugaba da zai tsayar musu da hadin kansu, kuma ya gyara musu Al'amuransu, sannan yayi musu wasiyya da tsoron Allah da kuma wadanda suke tare da shi Alkairi, kuma ya shiryar da su zuwa ga Abinda ya wajaba akansusubi game da abinda ya kamata suyi da abokan gaba, su guji shishigi da kuma yaudara da kuma Musla, da kuma kashe wanda bai balaga ba, kuma ya wajaba su fara kiran Mushrikai zuwa Musulunci, idan suka amsa hakan to su kwadaitar da su zuwa Hijira zuwa garin Musulmi, kuma su sanar da su cewa suna da duk hakkin da wadanda sukai hijira kafinsu suke da shi to tdan suka ki hijira to sai ayi musu hukuncin larabawan kauye