Manzon Allah ya kasance yana cikin shirin Jahadi, kuma ya dau duk matakansa, saboda fadin Allah Madaukakin Sarki: “Ku tanadi shirin Karfi gwargwadon ikonku, na karfin kamar Daurarrun Dawakai da zaku tsorata Makiyan Allah da Makiyanku das u” saboda haka ya kasance, yana horar da dawakai da juriyar yinwa, kuma yana gogar da Sahabbansa kan gasar gudu a kansu don su koyi hawansu, da kai hari da kuma bara, kuma yana nuna musu gwargwadon inda horarren Doki zai iya kaiwa a guje, da wanda ba horarren ba -Kuma su ne Dawakan da akai Musu Horan yinwa da daidaitawa har sukai Karfi- gwargwadon abunda zaikai Mil shida, wanda kuma ba’a yi musu horon ba Mil daya, Abdullahi Bn Umar –Allah ya yarda das hi- ya Kasance daya ne daga cikin Samarin Sahabbai wadan da suke yin hakan.