Yayin da Allah yai budi ga Manonsa na ganimomi masu yawa a yakin Hunain kuma bayan ya bar takunkumin da ya sanywa Ta'if kuma sai ya dawo mata da wasu ganimomi kuma maf yawan su Dabbobi ne kuma sun kai sama da Rakumi Dubu arba'in da da Dari da Ashirin na Dabbobisai Annabi ya bawa wasu Mutane sababbin shiga Musulunci don ya jawo hankalinsusai wasu daga cikin Mutanen Madina abun bai musu dadi ba amma manyan cikin su sun san ewa yadda Annabi yayi shi gaskiya yayin da Maganar su ta isar masa lokacin da wasu suka ce Annabi ya badaganima ga Mutanen da takubbunan mu suke digar jini daga yakarsu sannan ya kyale mu sai Annabi yayi umarnin da a tara su a wani wuri da ake kira kubba sai suka taru sai ya ce musu ya isarmun maganganun wasunku. har zuwa karshen abinda suka ce sai yai musu fada kuma sannan ya yi ikirari gare su abinda suka gabatar masa na taimako da kuma taimakonsu ga Musulunci da ya zo da shi sai ransu yayi dadi kuma suka san abu mai girma da Allah ya tanadar musu na zama da Annabinsa, da kuma dawowarsu tare da shi cikin tawagarsu, bugu da kari da abinda ya tanadar musu na ladan lahirasabida abinda suka gabatar na bajinta, sai Annabi ya Umarce suda hakuri akan abinda zai same su bayansa na juya musu baya. Taisir (306) tanbih Al'afham(3/403) Ta'asis Al'ahkam 93/197