Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance a zaune a cikin wasu jama'a cikin sahabbansa, daga cikinsu akwai Abubakar da Umar, sai (Annabi) - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya miƙe sannan ya ɗan jinkirta bai gare dawo ba, sai suka ji tsoron kada ya gamu da wani mummunan abu cikin maƙiyi; kodai ribacewa ko waninsa. Sai sahabbai - Allah Ya yarda da su - suka miƙe a firgice, farkon wanda ya fara firgita shi ne Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - har ya je wata gona ta Banu Najjar, sai ya fara kewayata wataƙila ya samu wata buɗaɗɗiyar ƙofa bai samu ba, sai dai ya samu wata 'yar ɓula (kafa) ƙarama a cikin garu wacce ruwa zai shiga daga gare ta , sai ya takure jikinsa har ya shiga sai ya samu Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce masa: Kaine Abu Huraira? Ya ce: Eh. Ya ce: Meke damunka? Sai Abu Huraira ya ce: Ka kasance kana cikimmu, sai ka miƙe sai kaɗan jinkirta ba mu ganka ba, sai muka ji tsoron mu rasaka, sai muka firgita, na kasance ni ne farkon wanda ya firgita, sai na zo wannan shingen, sai na yi gaggawa kamar yadda dila yake yin gaggawa, alhali waɗannan mtanen suna bayana. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ba shi takalmansa alamar cewa shi mai gaskiya ne, kuma ya ce da shi: Ka tafi da takalman nan nawa waɗannan, duk wanda ka gamu da shi a bayan wannan shingen yana shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah, kuma zuciyarsa ta sakankancewa da shi; duk wanda siffarsa ta zama haka to shi yana daga cikin 'yan aljanna. Farkon wanda ya fara gamuwa da shi shi ne Umar, sai ya ce da shi: Waɗannan waɗane takalma ne ya Abu Huraira? Sai ya ce: Waɗannan takalaman manzon Allah ne - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aikoni da su cewa duk wanda na gamu da shi yana shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah zuciyarsa tana mai sakankancewa da haka, to in yi masa albishir da aljanna. Sai Umar ya daki ƙirjin Abu Huraira da hannunsa sai ya faɗi ta bayansa, sai ya ce: Ka koma ya Abu Huraira, sai na dawo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a firgice fuskarsa ta canja yana shirin yin kuka, kuma Umar ya bini ya tafi a bayana. Sai (Annabi) - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Me yasameka ya Abu Huraira? Na ce: Na gamu da Umar, sai na ba shi labarin abinda ka aikoni da shi, sai ya dakeni duka ɗaya har na faɗi ta bayana, kuma ya ce: Ka koma. Sai (Annabi) - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ya Umar, Me yasa ka aikata haka? Sai Uamr ya ce: Ya manzon Allah, fansarka babana da babata, shin ka aiki Abu Huraira da takalmamnka cewa wanda ya shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah zuciyarsa tana mai sakankancewa da hakan cewa ya yi masa albishir da aljanna? Ya ce: Eh. Ya ce: To kada ka aikata, domin cewa ni ina jin tsoron kada mutane su dogara akan faɗinta kawai ba tare da aiki ba, ƙyalesu su yi aiki. Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: To ka ƙyalesu.