explain-icon

Explanation

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana cewa rangwame da sauƙi da bi-sannu - sannu a magana da aiki suna ƙarawa abu kyau da cika da ƙaye, kuma nan ne ya fi cancanta mutum ya samu buƙatarsa. Rashin sassauci yana aibanta lamura yana muzanta su, kuma yana hana mai hakan cimma buƙatarsa, in kuma ya samu, to, da baƙar wahala ne.

explain-icon

Benefits from the Hadith

  • Kwaɗaitarwa a kan ɗabi’antuwa da halin sauƙaƙawa.
  • Sauƙaƙawa tana ƙawata mutum, ita ce dalili na alheran duniya da lahira.