Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, lallai cewa ni hakika na aikata dukkanin zunubai da sabo, ban bar wani karamin laifi ba ko babba sai da na aikata shi , shin za'a gafarta mini? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce masa: Shin baka shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ba ?? kuma Muhammad Manzon Allah ne? Ya maimaita masa sau uku. Sai ya amsa masa: Eh ina shaidawa, Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata gare shi - ya ba shi labarin falalar shahada biyu, da kuma kankarewarta ga munanan laifuka, kuma lallai cewa tuba yana kankare abinda ke kafinsa.