Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya mutu kuma ya gamu da Allah yana mai kaɗaita Allah ba ya hada wani da abu da shi to shi yana daga cikin 'yan aljanna, ko da an yi masa uƙuba da zunubinsa a cikin wuta. Wanda ya mutu alhali yana hada wani abu da shi to wani kyakkyawan aiki ba zai yi amfani tare da shirkarsa ba; kuma aljanna haramun ce gare shi .