Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance a wata tafiyarsa a lokacin mutane suna wurin baccin su inda suke bacci a bukkokinsu da shemominsu. Sai ya aika wani mutum don ya sami mutane ya umarcesu da yanke kowanne abu da aka rataya a wuyan raƙumi, shin na tsirkiya ne, ko wani abu kamar ƙararrawa ko takalmi, domin sun kasance suna yi musu rataye saboda tsoron kambun baka, sai aka umarce su da su yanke, domin babu abin da take karawa, kuma anfanarwa da cutarwa suna hannun Allah ne Shi kadai.