Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fita zuwa Hunain shi: Wani kwari ne tsakanin Makka da Da’if, Ya kasance a tare da shi akwai wasu daga sahabban da ba su dade da shiga Musulunci ba. sai suka wuce wata bishiya ana ce mata: "Ma'abociyar rataya", wato: Ma'abociyar rataye-rataye, mushirikai sun kasance suna girmamata kuma suna rataya makamansu akanta da wasunsu dan neman albarka (sa’a). sai suka nema daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanya musu wata bishiyar irinta, za su dinga rataya makamansu akanta, dan neman albarka (sa’a), Dan zatonsu cewa wannan al'amarin ya halatta, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi tasbihi dan inkarin wannan maganar, da kuma girmama Allah, kuma ya sanar da cewa wannan maganar ta yi kama da maganar mutanen (Annabi) Musa da suka ce da shi: {Ka sanya mana wani ubangiji kamar yadda suke da iyayen giji}, lokacin da suka ga wanda yake bautawa gumaka sai suka nemi ya zama suna da gumaka kamar yadda mushrikai suke da gumaka, kuma cewa wannan bin hanyar hanyarsu ne, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bada labarin cewa wannan al'ummar za ta bi hanyar Yahudawa da Nasara kuma za ta aikata irin aikinsu, dan gargadarwa akan hakan.