Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana hani daga rantsuwa da ɗawagitai, jam'ine na dagutu, sune gumakan da mushrikai suke bauta musu koma bayan Allah, sune sababin shisshiginsu da kafircinsu, kuma tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana yin hani daga rantsuwa da iyaye; inda ya kasance daga al'adar larabawa a Jahiliyya shi ne su yi rantsuwa da iyayensu dan alfahari da girmamawa.