Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Zai cewa mafi ƙanƙantar 'yan wuta a zaba bayan shigarta: Da ace duniya da abinda ke cikinta nakane shin zaka fanshi kanka da ita daga wannan azabar? Sai ya ce: Eh, Sai Allah Ya ce: Haƙiƙa Na nema daga gareka kuma Na umarceka da mafi sauƙi daga hakan lokacin da aka karɓi alƙawari gareka alhali kai kana cikin tsatson (annabi) Adam da kada ka yi shirka daNi da wani abu; sai kaƙi lokacin da Na fitar da kai zuwa duniya sai dai shirka.