Nana A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗa a cikin rashin lafiyarsa wacce ta tsananta gare shi kuma ya mutu a cikinta: Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, Ya koresu daga rahamarSa; hakan domin cewa su sun riƙi ƙaburburan Annabawansu a matsayin masallatai. Ta hanyar yin gini a kansu ko yin sallah a wurinsu ko zuwa garesu (kallonsu). (Nana A'isha) Allah Ya yarda da ita ta ce: Da badan wannan hanin da gargaɗin daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da tsoron sahabbai kan abinda za’a yi wa ƙabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kamar yadda Yahudawa da Nasara suka yi wa ƙaburburan Annabwansu ba da anbayyanar da ƙabarinsa kuma an fito da shi.