Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - yana ruwaito wani yanki daga siffar sallar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, yana ba da labarin cewa ya kasance idan ya tashi yin sallah yana kabbarar harama a yayin da yake miƙewa, sannan ya yi kabbara a yayin da yake cirata zuwa ruku'u, da yayin da yake yin sujjada, da yayin da yake ɗago kansa daga sujjada, da yayin da yake yin sujjada ta biyu, da yayin da yake ɗago kansa daga gareta, da yayin da yake miƙewa daga raka'a biyun farko bayan zama don tahiyar farko a sallah mai raka'a uku ko huɗu, sannan ya aikata hakan a dukkanin sallah har sai ya gamata, ya kasance yana cewa a yayin da ya ɗago bayansa daga ruku'u: Allah Ya ji wanda ya gode maSa, sannan ya ce alhalin yana tsaye: Ya Ubangijimmu godiya ta tabbata a gareKa. Sannan Abu Huraira yake cewa a yayin da ya idar da sallar: Na rantse da wanda raina yake a hannunSa, lallai ni ne mafi kusancinku kamaceceniya da sallar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wannan ita ce siffar sallarsa har ya bar duniya.