Wasu mutane sun zo wa ɗaya daga sahabbai suna tambayarsa game da minbarin Annabi wanda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya riƙeshi: Da me aka yi shi? Haƙiƙa sun yi jayayya a hakan, sai ya ambata musu cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya aika zuwa ga wata mata daga Mutanen Madina tana da wani yaro kafinta, sai ya ce da ita: Ki umarci yaronki ya yi min minbarin da zan zauna a kansa lokacin da zan yi wa mutane magana, sai matar ta amsa, ta umarci yaronta ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - minbari na bishiyar Ɗarfa'u, lokacin da ya gama sai matar ta aika da munbarin zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya yi umarni da shi sai aka ajiye shi a wurinsa a masallaci, sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi sallah a kansa ya yi kabbara alhali yana kansa, sannan ya yi ruku'u alhali yana kansa, sannan ya sauka yana tafiya ta baya, ba tare da ya juyo da fuskarsa ba zuwa ta baya ba, sai ya yi sujjada a asalin minbarin sannan ya dawo, lokacin da ya gama sallar sai ya fuskanci mutane, ya ce: ya ku mutane, kaɗai na aikata haka ne don ku yi koyi kuma ku san sallata.