Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya kasance yana ɗaga hannayensa agurare uku a sallah, daura da kafaɗa wanda shi ne: Matattarar ƙashin kafaɗa da damtse. Guri na farko: Idan zai buɗe sallah yayin kabbarar harama. Na biyu: Idan Zai yi kabbara dan ruku'u. Na uku: Idan ya ɗago kansa daga ruku'u kuma ya ce: Allah Ya ji wanda ya gode maSa, Ya Ubangijinmu godiya ta tabbata gareka. Ya kasance ba ya ɗaga hannayensa a lokacin fara sujjada, ko lokacin ɗagowa daga sujjada.