Ya kasance cikin koyarwar Manzon Alllah SAW idan ya tashi daga Raka'ar farko zuwa ta biyu, da ta Uku zuwa ta Hudu baya tashi har sai ya tabbata a zaune zama takaitacce, sannan ya ya tashi, kuma wannan zaman ana kiransa da zaman Hutawa, kuma haqiqa Adadin Sahabbai da yawa sun rawaito hakan