Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa Allah Ya umarce shi a yayin sallah ya yi sujjada akan gabbai bakwai na jiki; su ne: Na farko: Goshi: Shi ne: Fatar fuska a saman hanci da idanuwa, Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi nuni zuwa hancinsa, yana mai bayyana cewa goshi da hanci gaba daya ce daga bakwan, da kuma karfafa cewa mai sujjada yana shafar kasa da hancinsa. Gaba ta biyu da ta uku: Hannaye. Ta hudu da ta biyar: Gwiwoyi. ta shida da ta bakwai: 'Yan yatsun diga-digai. Kuma ya umarcemu kada mu daure gashin mu, ko mu tattaro tufafinmu sashinsu akan sashi a yayin sujjada akan kasa dan karesu; kai ya sake su har su sauka a kasa, sai ka yi sujjada tare da gabbai.