Wanna Hadisin yana bayanin hanyar da ake saukowa don yin Sujada, kuma ita ce cewa zai sanya Hannayensa kafi guiwoyinsa, wasu kuma Hadisan suka zo da saukowa da Guiwoyi kafin Hannaye, to baki xayan Al-amuran biyu sun halatta ba za'a ga laifin wanda yayi su ba