Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana neman tsarin Allah daga abubuwa hudu bayan tahiyar karshe kuma kafin sallama a sallah, ya kuma umarcemu mu nemi tsarin Allah daga garesu, Na farko: Daga azabar kabari. Na biyu: Daga azabar wuta hakan a ranar Alkiyama . Na uku: Daga fitinar rayuwa na sha'awowin duniya haramtattu da kuma shubuhohi masu batarwa, da kuma fitinar mutuwa, wato lokacin fitar rai, na karkacewa daga musulunci ko sunna, ko fitinar kabari kamar tambayar Mala'iku biyu. Na hudu: Fitinar mai yawan yawo makaryaci (Dajjal) wanda zai fito a karshen zamani, Allah zai jarrabi bayinSa da shi, ya kebance shi da ambato dan girman fitinarsa da batarwarsa.