Wannan Hadisin yana bayanin Sigar Tahiya, kuma cewa Annabi SAW ya Kasance yana kwaxayin koyar da su kamar yadda yake koya Musu Al-qurani, kuma sigar ita ce: "Gaisuwoyi Masu Albarka, Salatai maisu tsarki ga Allah, Amincin a gareka Manzon Allah da rahamatullah da Albarkatansa, Amincin Allah a garemu da sauran bayin Allah Salihai, na Shaida babu wani abun bautawa da gaskiya sai Allah, kuma na Shaida cewa Annabi Muhammadu Manzon Allah ne" kuma tayi kama da sigar Tahiyar nan Mashahuriya da ta zo daga Ibn Mas'ud -Allah ya yarda da shi- kuma cewa Banbancin Qarin Albarkatun, kuma shafe waw din a cikin kalmomi biyu bayanta, kuma ya halarta banbantawa tsakanin Sigogin da suka zo a Tahiya