Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya yi kabbarar sallah yana yin shiru kaɗan kafin ya karanta fatiha, yana buɗe sallarsa da wasu daga addu'o'i a cikinta, daga abinda ya zo daga waɗannan addu'o'in faɗinsa: "Ya Allah Ka nesanta tsakanina da kurakurai na kamar yadda Ka nesanta tsakanin mahudar rana da mafaɗarta, Ya Allah Ka tsaftace ni daga kurakuraina kamar yadda ake tsaftace farar tufa daga datti, ya Allah Ka wanke ni daga zunubai na da ruwa da ƙanƙara da ruwa mai tsananin sanyi". Shi yana roƙon Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya nisantar da tsakaninsa da kurakurai da kada ya faɗa cikinsu, nisantarwa ta inda gamuwa ba zata ƙara faruwa tare da shi ba, kamar yadda babu haɗuwa tsakanin mahudar rana da mafaɗarta har abada, idan kuma ya faɗa cikinsu to Ya tsaftace su Ya kawar da su kamar yadda ake kawar da datti daga farin tufa, kuma Ya wanke shi daga kurakuransa Ya sanyaya horuwarsu da zafinsu, da waɗannan masu tsaftacewar masu sanyi: Ruwa, da kankara, da sanyi.