Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - tana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - lokacin da aka saukar masa da: {Idan nasarar Allah ta zo da buɗi} ya fassara Alƙur'ani kuma ya yi gaggawa zuwa ruko da umarnin Allah - Maɗaukakin sarki - a cikin faɗinSa: {Ka yi tasbihi da godiyar Ubangijinka kuma ka nemi gafararSa}, to ya kasance yana yawaita faɗa a cikin halin ruku'insa da sujjadarsa a tsakiyar sallah: "Tsarki ya tabbatar maKa" da tsarkakewa gareKa daga dukkan tawaya daga abinda ba ya dacewa da Kai, "Ya Allah Ubangijinmu da godiyarKa" da yabo abin yabo gareKa dan cikar zatinka da siffofinKa da ayyukanKa, "Ya Allah Ka gafarta mini' Ka shafe mini zunubina Ka ƙetare daga gare shi .