Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana cewa idan ya kammala sallarsa; Ina neman gafar Allah, Ina neman gafarar Allah, Ina neman gafarar Allah. Sannan sai ya girmama Ubangijinsa, ya ce: "Ya Ubangiji Kai ne aminci, kuma aminci daga gareKa yake, Ka girmama ya ma’abocin girma da karamci". Shi Allah tsarkakke ne, kuma cikakke ne a siffofinsa, kuma Ya tsarkaka daga barin kowanne aibu da tawaya, kuma ka nemi waraka daga dukkan sharri duniya da lahira daga wajenSa ba daga wani ba, Shi Allah alheranSa sun yawaita a duniya da lahira, Ma’abocin girma da kyautatawa ne.