Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na kasance ina barci a gefen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai na rasashi da daddare, sai na laluba da hannayena gurin da ya kasance yake sallah a cikinsa a cikin ɗaki; sai gashi yana sujjada alhali diga-digansa suna a tsaye, sai gashi shi yana cewa: (Ina neman tsari) ina kamun ƙafa (da yardarKa daga fushinKa) akaina ko akan al'ummata, (kuma) ina neman tsari (da rangwaminKa) afuwarKa mai yawa (daga uƙubarKa), (Ina neman tsari daga gareKa) da siffofin kyawunKa daga siffofin ɗaukakarKa, inda ba mai fakewa daga gare Ka sai Kai, babu matserata kuma babu mafaka daga Allah sai dai zuwa gareShi, (Ba zan iya ƙididdige yabo a gareKa ba) ba zan iya kuma bazan kai ƙololuwa a lissafewa ba da kuma ƙirgawa ba saboda gajiyawata ba, ƙididdige ni'imarKa da kyautatawarKa kamar yadda Kake cancantarsa ba koda na yi ƙoƙari a hakan. (Kai kamar yadda Ka yabi kanKa) Kaine wanda Ka yi yabo akan zatinKa yabon da ya dace da Kai, waye yake da iko akan bada haƙƙin yabonKa?!