Sahabbai sun tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da siffar salati gare shi? bayan sun san siffar sallama gare shi a Tahiya: "Aminci ya tabbata agareka ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarSa..."? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar da su siffar salati gare shi, ma'anarsa: "Ya Allah ka yi salati ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad" Wato: Ka yi yabo gare shi da ambato mai kyau a cikin jama'a madaukaka, da mabiyansa a cikin AddininSa, da muminai daga makusantansa. "kamar yadda Ka yi salati ga (Annabi) Ibrahim" Kamar yadda ka yi baiwa ga iyalan (Annabi) Ibrahim - aminci ya tabbata agare shi - su ne (Annabi) Ibrahim, da (Annabi) Isma'il, da (Annabi) Ishak, da zuriyarsu da mabiyansu muminai, to ka riskar da falalararKa ga (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -. "Lallai kai abin yabo ne kuma Mai girma" Wato: Abin yabo a zatinKa da siffofinKa da ayyukanKa, Mayalwaci a girmanKa da sarautarKa da baiwarKa. "Ya Allah Ka yi albarka ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad kamar yanda ka yi albarka ga Ibrahim" Wato: Ka ba shi alheri da girmamawa mafi girmasa Ka kara masa Ka tabbatar masa.