Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da ganawar Allah ga bawanSa mumini ranar alƙiyama, sai ya ce: Za'a kusanto da mumini ranar alƙiyama daga Ubangijinsa sai Ya sanya suturarSa daga ma'abota wurin tsayuwa har ya zama waninsa ba zai yi tsinkaye akan sirrinsa ba, sai ya ce masa: Shin kana sanin zunubi kaza da kaza... Zai tabbatar masa da zunuban da suke tsakanin bawa da UbangijinSa. Sai ya ce: Na'am Eh, ya Ubangiji. Har idan mumini ya firgita ya ji tsoro, sai Tsarki ya tabbatar maSa Ya ce masa: Lallai cewa Ni na suturta su gareka a duniya, kuma cewa Ni na gafartasu gareka a yau, sai a ba shi takardar kyawawan ayyukansa. Amma kafiri da munafuki sai a yi kira a gabn mahalarta: Waɗannan sune waɗanda suka yi wa Ubangijinsu ƙarya, ku saurara tsinuwar Allah ta tabbata akan azzalumai.