Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa a cikin aljannar Lahira akwai darajoji da matsayi ɗari, tsakanin kowace daraja a nisa kamar tsakanin sama da ƙasa ne, kuma mafi ɗaukakar waɗanan aljannatan ita ce aljannar Firdausi, daga nan ne ƙoramun aljanna huɗu suke ɓuɓugowa, a saman Firdausi ne al’Arshi yake; idan zaku roƙi Allah to ku roƙe Shi Firdaus; saboda ita ce a saman dukkaninl aljannatan.