explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci Ali ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya roƙi Allah ya tambaye shi sai ya ce: (Ya Allah Ka shiryar da ni) Ka shiryar da ni Ka nuna mini (Ka datar da ni) Ka yi mini gam da katar, Ka sanya ni madaidaici a dukkan al'amurana. Shiriya: Ita ce sanin gaskiya a fayyace kuma a dunƙule, da dacewa ga binta a zahiri da baɗini. Dacewa kuwa: Ita ce dacewa da daidaita a dukkanin al'amura da abinda zai zama daidai akan gaskiya, shi ne hanya madaidaiciya a magana da aiki da ƙudiri. Kuma cewa umarni na ma'ana yana bayyana da abin ji; ka tina alhali kai kana yin wannan addu'ar cewa: (Shiriya: Shiriyarka (irin ta) hanya) ka halarto zuciyarka alhali kai kana roƙon shiriya kamar shiriyar wanda ya yi tafiya, cewa shi baya kaucewa akan hanya dama da hagu; hakan dan ya kuɓuta daga ɓata (makuwa), da haka ne zai samu kuɓuta, ya kai zuwa manufarsa a gaggauce. (Daidaita: (irin) daidaitar kibiya) kai kana lura a lokacin da kake daidaita kibiya a gaggawar saduwarta da samunta ga inda aka harbata, mai harbi idan ya harbi inda yake so sai ya daidaita kibiya wajen inda zai harba, to haka nan zaka roƙi Allah - Maɗaukakin sarki - cewa abinda ka yi niyyarsa na daidai yana kan yanayin kibiya; sai ka zama a roƙonka mai neman matuƙar shiriya, da ƙarshen daidaita. Ka halarto wannan ma'anar a zuciyarka har sai ka roƙi Allah daidai dan abinda ka yi niyyarsa daga hakan ya zama akan yanayin abinda kake anfani da shi na harbi.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Mai addu'a ya kamata ya yi kwaɗayi akan daidaita aikinsa da daidaita shi ta hanyar lazimtar sunna da tsarkake niyya.
  • An so yin addu'a da waɗannan kalmomin mai tattarowa ga dacewa da daidaita.
  • Ya kamata ga bawa ya nemi taimakon Allah - Maɗaukakin sarki - a dukkan al'amuransa.
  • Buga misali a lokacin koyarwa.
  • Haɗawa tsakanin neman shiriya da gyaruwar hali, da tafiya akansa da rashin karkata daga gare shi koda ƙiftawar ido da gyaruwar makoma, faɗinsa: "Ka shiryar da ni" shi ne ya zama mai tafiya akan hanyar shiriya, da faɗinsa: "Ka datar da ni": Na dacewa da rashin karkacewa a lokacin shiriyar da ya riƙeta.
  • Mai Addu'a ya kamata gare shi ya himmantu da addu'arsa, ya halarto ma'anonin addu'arsa a cikin zuciyarsa; to wannan ya fi kusa ga karɓuwa.