An rawaito daga Shakl Bn Humaid -Allah ya yarda da shi- Na ce: Ya Manzon Allah ka koyamun wata Addu'a ya ce kace: "Ya Ubangiji ina neman tsarinka daga sharrin jina, da kuma sharrin Ganina, da kuma Sharrin Harshena, da kuma Sharrin Zuciyata, da kuma Sharrin farjina" Ingantacce ne - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi