Ya kasance daga addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance yana cewa: (Ya Allah gareKa ne na miƙa wuya) kuma na jawu, (da Kai ne na yi imani) na gasgata kuma na yi iƙrari, (kuma gareKa ne na dogara) na fawwala na kuma dogara, (gareKa ne na koma) na koma na fuskanta, (saboda Kai ne na yi husuma) na yi jayayya da maƙiyanKa, (Ya Allah ni ina neman tsarinKa) ina fakewa (da buwayarKa) da hanawarKa da kuma rinjayenKa, (babu abin bautawa da gaskiya sai Kai) kuma babu wani abin bautawa da gaskiya inba Kai ba, (da Ka ɓatar da ni) daga shiriya da dacewa da yardarKa, (Kai ne Rayayye wanda ba zai mutu ba) kuma ba zai ƙareba, (aljanu da mutane kuwa zasu mutu).