explain-icon

Bayani

Ya kasance daga cikin addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: (Ya Allah lallai ni ina neman tsari) ina fakewa (da Kai) banda waninKa, (daga munanan) abubuwan da Allah da ManzonSa suka hana su, (ɗabi'u) kamar ƙullata da hassada da girman kai, (da kuma) munanan (ayyuka) kamar zagi, (da) dukkanin (soye-soyen zuciya), waɗanda zuciya take son su alhali sun saɓawa shari'a.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Falalar wannan addu'ar kuma an so a yi ta.
  • Mumini yana kwaɗayi akan nisantar ɗabi'u ababen zargi da kuma munanan ayyuka, kuma yana kiyayewa daga bin son rai da kuma afkawa cikin sha'awowi.
  • Rarrabuwar ɗabi'u da soye-soyen zuciya zuwa munana da kuma kyawawa.