Wani bawa wanda mai shi ya ɗorawa fansa kuma ya yi ittifaƙi tare da shi akan ya sayi kansa ya 'yantata dan ya zama ɗa, kuma ba shi da dukiya, ya zo wurin sarkin muminai Aliyu ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - sai ya ce: Haƙiƙa ni na gajiya (na kasa) daga biyan abinda ke kaina to ka taimakeni akan biyansa da dukiya, ko da koyarwa da shiryarwa, sai sarkin muminai ya ce masa; Shin bana sanar da kai wasu kalmomi ba waɗanda manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar dani su, da a ce a kanka akwai bashi kwatankwacin wani dutse mai suna Seer na ƙabilar Ɗayyu ne da Allah Ya biya maka shi zuwa ga mai shi, kuma Ya tsamoka daga ƙasƙancinsa, Ya ce: Ka ce: (Ya Allah Ka isar mini) Ka juyar mini Ka nisantar da ni (da halal ɗinKa) ina mai wadatuwa da ita, (daga) faɗawa a (haram ɗinKa), (Kuma Ka wadatar da ni) Ka isar mini (da falalarKa) samuwarKa (daga wanda ba Kai ba) cikin halitta.