Da Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Ka nemi tsari da Allah daga Wahalar Bala'i, da Fadawa tabewa, da Mummunan Rabo, da Kuma Dariyar Makiya" kuma cikin wata Riwayar Sufyan Al-Sauri ya ce: Ina kokwanton ni na kara daya daga cikin su. Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi