Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi rantsuwa akan cewa kofunan tafkinsa a ranar Alkiyama sun fi yawan adadin taurarin sama, Wannan yana bayyana a cikin dare mai duhun da babu wata a cikinsa; domin kuwa dare mai wata taurari ba sa kasancewa a bayyane a cikinsa dan boyuwarsu da hasken wata, kuma wacce babu hazo a cikinta; domin samun hazo yana hana ganin taurari, Kuma cewa kofunan Aljanna, wanda ya sha daga abin shan dake cikin su ba zai yi kishirwa ba har abada, kuma wannan yana kasancewa karshen abinda yake samun mai shan na kishirwa. Kuma cewa tafkinsa indararo biyu daga Aljanna suna zuba a cikinsa, kuma fadinsa tamkar tsawonsa ne; Tafkin madaidaicin rukunai ne, tsawonsa yana kasancewa gwargwadan tazarar dake tsakanin Amman -ita wani gari ne a Balka'a daga Sham-, zuwa Ailata, wani birni ne sananne a gefen Sham. Ruwan tafkin ya fi nono fari, kuma dandanonsa ya fi zuma zaki.