Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin farkon jama'a ta muminai waɗanda zasu shiga aljanna fuskokinsu suna kan surar wata daren goma sha huɗu a haske, sannan masu biye musu suna kan surar tauraro mafi tsananin haske, kuma suna da wasu siffofin cika inda ba sa fitsari ba sa bahaya, kuma ba sa tofar da yawu kuma ba sa tofar da majina, abubuwan taje kansu shi ne zinare, kuma guminsu shi ne almiski. Kuma abin kunna tiraren wutarsu yana tada ƙanshi mafi daɗin ƙanshin tirare kuma mafi ƙanshin tiraren wuta, kuma matansu sune Hurul inu, halittarsu akan halittar mutum ɗaya ne akan surar babansu Annabi Adam a tsawo da kuma halitta; tsawon jikinsa zira'i sittin ne a sama.