Wani mutumin karkara irin waɗanda suke zama a sahara ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: game da lokacin tashin alkiyama? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi Ya ce masa: Meka tanadar mata na aiki na gari? Sai mai tambayar ya ce: Ban tanadi wani aiki mai yawa ba sai dai ni ina son Allah da ManzonSa, bai ambaci wanin hakan ba daga ayyuaka na zuciya da jiki da dukiya; domin su dukkaninsu rassa ne ga soyayya masu jerantuwa ne akanta, kuma domin soyayya ta gaskiya tana zaburar da kokarin yin aiki na gari. Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi Ya ce masa: Lallai kai kana tare da wanda ka so a aljanna. Sai sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suka yi farin ciki mai girma da wannan busharar. Sannan Anas ya bada labarin cewa shi yana son Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da Abubakar, da Umar, kuma yana kaunar ya kasance tare da su, koda aikinsa bai zama irin aikinsu ba.