explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wutar duniya wani yanki ne daga yanki saba'in daga wutar Jahannama, Wutar lahira karfin zafinta yana karuwa akan zafin wutar duniya da yanki sittin da tara, kowanne yanki daga gareta yana daidai da zafin wutar duniya. Sai aka ce : Ya Manzon Allah lallai cewa wutar duniya ta isa dan azabtar da masu shigarta. Sai ya ce: An fifita wutar Jahannama akan wutar duniya da yanki sittin da tara, kuma dukkaninsu tamkarta ne a cikin tsananin zafi.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Gargadarwa daga wuta dan mutane su nisanci ayyukan da zasu kai su zuwa gareta.
  • Girman wutar Jahannama da azabarta, da kuma tsananin zafinta.