explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa shi zai kasance a ranar Alkiyama akan tafkinsa dan ya ga wanda zai zo daga al'ummarsa zuwa tafkin, Kuma za'a rike wasu mutane a kusa da shi - aminci ya tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Ubangiji daga gareni ne kuma daga al'ummata ne, Sai a ce: Shin ka san abinda suka aikata bayan rabuwarka da su, wallahi ba su gushe ba suna komawa akan bayansu suna yin ridda daga addininsu, su ba sa tare da kai, kuma ba sa cikin al'ummarka.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Rahamar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa da kuma kwadayinsa gare su .
  • Hadarin sabawa abinda (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake akansa.
  • Kwadaitarwa akan riko da sunnar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.